Pinned post
A letter to my fellow Fulani tribesmen. Contrary to what Miyetti Allah thinks of herdsmen and nomadism in Nigeria.
@JaloAbba
Pinned post
An dawo da aikin gina babban ɗakin karatu na Ƙasa da ya kai Naira biliyan 155View quoted post on X
An sake dawo da aikin gina Babban ɗakin Karatu na Ƙasa (National Library of Nigeria) da ke Abuja, wanda ya kwashe shekaru ba a kammala ba.
Aikin, wanda aka fara a shekarar 2006, ya samu gudummawar Naira biliyan 25.6 daga masu hannu da shuni da suka amsa kiran Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, na mayar da kyaututtukan zagayowar ranar haihuwarta ta 65 ga kammala aikin.
Gwamnatin Tarayya za ta samar da sauran kuɗaɗen da ake buƙata. Daga cikin Naira biliyan 155 da aka ware, za a kashe Naira biliyan 118 wajen kammala ginin, yayin da Naira biliyan 37 za a yi amfani da su wajen samar da kayan aiki da kayan cikin ɗakin karatun.
Idan aka kammala, ɗakin karatun zai ƙunshi wuraren karatu da bincike, ayyukan samun bayanai ta hanyar fasahar zamani, wuraren baje koli da kuma sassa na musamman ga yara da masu buƙata ta musamman.
#ArewaForAsiwaju
#A4A
View quoted post on X